DH Hausa Tv
Mun buɗe wannan kafa ta DH Hausa TV domin kawo muku sahihan labarai masu inganci da suka shafi labaran duniya, wasanni da siyasa cikin gaskiya da ƙwarewa.
Ku kasance tare da mu domin samun ingantattun labarai a kowane lokaci. WhatsApp: 09030255151
18/09/2026
Dan wasa Christiano Ronaldo Ya Ci Gaba da Wakiltar Portugal, An Saka Sunansa Cikin Sabuwar Tawagar yan wasan Ƙasar.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
Fitaccen ɗan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo, zai ci gaba da buga wa ƙasar tasa wasa, bayan sabon kocin tawagar Portugal, Jorge Jesus, ya saka sunansa cikin jerin ’yan wasan da aka gayyata domin wasannin Nations League masu zuwa.
Wannan na nufin Ronaldo zai ci gaba da kasancewa cikin shirin tawagar ƙasar Portugal yayin da take tunkarar sabbin wasannin ƙasa da ƙasa.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
18/09/2026
NSCDC Ta Fara Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai 40 a Minna da ke jihar Neja.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
Hukumar NSCDC ta ƙaddamar da bincike kan mutuwar wasu mutane 40 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda s**a mutu yayin da suke tsare a hannun hukumar a Minna, Jihar Neja.
Hukumar ta ce binciken zai taimaka wajen gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen, da kuma tabbatar da matakan da s**a dace bisa doka.
Ana ci gaba da jiran cikakken bayani kan lamarin yayin da binciken ke gudana.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
18/09/2026
Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Kwamandan NSCDC na jihar Neja dake Najeriya Bayan Mutuwar Mutane 37 da a ke Tsare da su.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, bayan mutuwar mutane 37 da aka k**a bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da suke hannun hukumar.
Mutanen sun kasance cikin waɗanda jami’an NSCDC s**a k**a yayin samamen da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026 a yankin M.I. Wushishi/Lukoto na Minna.
Kwamandan ya ce an gano mutanen sun mutu ne bayan abin da aka bayyana a matsayin zargin ɓarkewar cuta, amma har yanzu ana gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce lamarin abin takaici ne, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike.
Haka kuma, NSCDC ta kafa kwamitin bincike domin duba yanayin mutanen lokacin k**a su, lokacin da s**a yi a tsare, yanayin wurin tsarewar da kuma kulawar lafiya da aka ba su.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
17/09/2026
AN SAKE GURFANAR DA WANI MATASHI A KOTU KAN ZARGIN CIN AMANA A HARKAR ALBASA.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta.
An sake gurfanar da wani matashi mai suna Gaddafi Hayin Gwarmai, ɗan asalin Bebeji, a gaban Kotun Majistare da ke Kafin Maiyaki, Kwanar Dangora, bisa zargin cin amana da ya shafi harkar saye da sayar da albasa.
A cewar bayanan da aka gabatar a kotun, ana zargin cewa an ba matashin kuɗi sama da Naira dubu ɗari (₦100,000) a wani ciniki na albasa, lamarin da ya jawo aka kai ƙara a kansa.
Masu gabatar da ƙara, PC Ishak da PC Aminu, sun gurfanar da shi a gaban kotu, inda aka karanta masa takardar tuhuma. Wanda ake zargin ya amsa tuhumar da aka karanta masa.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Alh. Isa, ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa Ranar Litinin, sannan aka tsare wanda ake zargin a hannun jami’in gidan ajiya da gyaran hali, Inspector Zakariya Abdullahi Kurawa, saboda ƙarancin lokaci.
Bayan fitowar daga kotu, wakilin DH Hausa TV, Dantala Uba Nuhu Kura, ya samu damar tattaunawa da wanda ake zargin.
Daga Dantala Uba Nuhu Kura.
DH Hausa TV
17/09/2026
Kotu majistiri da ke zaman ta a karamar hukumar kura a jihar Kano,
An Hukunta Wani Ɗan Acaba bisa Laifin Cin Zarafin Matar Aure a Kura.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta.
Wata Kotun Majistare da ke Ƙaramar Hukumar Kura a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Chief Magistrate Muhammad Alh. Isa, ta yanke wa wani ɗan acaba mai suna Jafaru hukunci bayan ya amsa laifin cin zarafin wata matar aure mai suna Gambo.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Jafaru ke jigilar matar daga Gundutse zuwa Tudun Bayaro, inda a cewar bayanan ƙarar, ya yi ƙoƙarin nuna mata sha’awarsa duk da ta bayyana masa cewa ita matar aure ce.
Daga bisani, lamarin ya kai ga aikata wani abu da ya jawo wa matar rauni, abin da ya sa aka kai ƙarar Jafaru gaban kotu.
Insifekta Nasiru Dansakkwato daga Ofishin ’Yan Sandan Kura ne ya gabatar da takardar tuhuma a gaban kotun.
Bayan Jafaru ya amsa laifinsa, kotun ta yanke masa hukuncin:
Watanni biyu a gidan gyaran hali, ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin bibiyar matar aure.
Watanni shida ko tarar Naira 40,000 kan laifin raunata ta.
Naira 35,500 a matsayin kuɗin maganin da matar ta kashe.
Bayan kammala shari’ar, an miƙa Jafaru ga jami’an gidan ajiya da gyaran hali domin aiwatar da hukuncin.
Rahoto Dantala Uba Nuhu Kura.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta
17/09/2026
A daidai wannan lokaci, ana ci gaba da zaman shari’ar da ake yi wa Malam Lawan Triumph a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu, Kano.
Ana gudanar da zaman ne a gaban kotun da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta.
Me zaku ce?
Daga naku HASSAN ABDULLAHI
17/09/2026
Bari Mu Ga Wanne Ne jama,a s**afi so a mulkin kasarnan A Cikinsu?
Daga naku HASSAN ABDULLAHI
kalma Daya tak akan wannan bawan Allah ?
16/09/2026
RANA DUBU TA ƁARAWO, RANA ƊAYA TA MAI KAYA wasu ’Yan Gida daya Sun Gurfana a Gaban Kotu majistiri Kan Zargin Satar Albasa a karamar hukumar bebeji da ke a Kano.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta.
Wasu ’yan gida ɗaya daya, ’yan asalin Gidan Baushe, a Ƙaramar Hukumar Bebeji, sun gurfana a gaban Kotun Majistare da ke Kafin Mayyaki, bisa zargin satar dashen albasa da aka ba su amana.
A cewar bayanan ƙarar, wani mai suna Babangida na Unguwar Rimi, Kwanar Dangora, ya ba su amanar yin dashen albasa a gonakinsa guda biyu.
Bayan albasa ta yi kyau, ana zargin sun haƙo wani ɓangare ba tare da izininsa ba, sannan s**a sayar da ita ga wani mutum, wanda shi ma aka haɗa cikin waɗanda ake zargin.
An ce darajar albasar da ake zargin an sayar ta haura ₦400,000.
Mai gabatar da ƙara, PC Aminu Muhimmancin Kwanar Dangora, ya gabatar da takardar tuhuma a gaban kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammad Alh. Isa.
Bayan karanta musu tuhumar, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa Litinin ta mako mai zuwa, domin ci gaba da shari’ar da kuma yanke abin da doka ta tanada. An kuma sanya waɗanda ake zargin a hannun Inspector Zakariya Abdullahi Kurawa.
Daga: Dantala Uba Nuhu Kura.
DH Hausa TV | Labarai Masu Nagarta.
BIDIYO: Yadda wasu ƴan Najeriya s**a fara barkwanci bayan sayan hannun jari na IPO daga matatar mai ta Dangote.
Daga naku HASSAN ABDULLAHI
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
Danhassan Town Kura Local Government
Kano