Dr Ayman muhd Sareena
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dr Ayman muhd Sareena, Health/Beauty, Kano State Nigeria � Garko local Government Sareena, Kano.
10/09/2026
Sojan Arewacin Najeriya da Ya Birge Sarauniya Elizabeth, Har Aka Ɗaga Masa Matsayi
Wannan labari ne mai ban sha’awa game da Major Bulama Biu, wani fitaccen soja ɗan Najeriya, wanda aka haife shi a ranar 15 ga Maris, 1934, a garin Biu da ke jihar Borno. Ya shiga aikin sojan Najeriya a ranar 5 ga Fabrairu, 1952.
A lokacin da Sarauniya Elizabeth II ta Birtaniya ta kai ziyara Najeriya, Bulama Biu na cikin sojojin da aka shirya domin karɓar sarauniyar tare da faretin sojoji.
A lokacin da yake tsaye cikin jerin gwanon sojoji, wani abu da bai yi tsammani ba ya faru. Sarauniyar ta lura da shi kuma ta burge da yadda ya tsara kayan aikinsa na soja. An bayyana Biu a matsayin ɗaya daga cikin sojojin da s**a fi kyau wajen shiryawa da sanya kayan faretin. Daga bisani, bisa ga wannan labari, an ɗaga masa matsayi zuwa Corporal (Kofur).
Ba a nan labarin ya tsaya ba. Bayan wani lokaci, Biu ya sake samun karin girma zuwa Sergeant (Sajan) bayan ya yi fice a wani atisayen yaƙi na bataliya da aka gudanar a 44 Battalion, Kaduna.
Yayin da yake ci gaba da gudanar da aikinsa a sabon matsayinsa, an tura shi wata muhimmiyar tawaga zuwa Congo, domin aikin ceto wani jami'in Birtaniya. Tawagar ta yi nasara wajen kammala aikin, kuma saboda bajintar da ya nuna, Biu ya sake samun karin girma zuwa Staff Sergeant.
A shekarar 1964, Major Bulama Biu ya zama RSM (Regimental Sergeant Major) na farko a tarihin Nigerian Defence Academy (NDA). A wannan matsayi, ya taka muhimmiyar rawa wajen horar da jami'an soja, har da waɗanda s**a shiga cikin Regular Courses 1 zuwa 21.
A shekarar 1977, an ba shi commission, inda ya zama Captain (Kyaftin), sannan aka tura shi Depot Nigerian Army Training School, Zaria. A can ne ya zama shugaban Nigerian Drill School, inda ya ci gaba da koyar da sojoji dabarun faretin soja da ladabtarwa.
Daga bisani aka ƙara masa girma zuwa Major, kuma ya riƙe matsayin Commanding Officer-in-Charge of Drill a Nigerian Army School of Infantry (NASI), Jaji.
Saboda irin gudummawar da ya bayar ga
10/09/2026
KUƊI DA DUKIYOYIN DA AKA CE MARIGAYI
الدنيا؟
ALHAJI AMINU DANTATA YA BARI A DUNIYA An ce ya bar kuɗi har naira tiriliyan 61 a bankunan Najeriya da na ƙasashen waje.
Haka kuma, an ce ya mallaki gidajen sayar da man fetur (filling stations) guda 800 a ciki da wajen Najeriya, waɗanda ba sa ɗauke da sunansa amma mallakinsa ne.
A jihar Kano kaɗai, an ce ya bar gidaje guda 500, tare da filaye 1,200 waɗanda aka yi musu katanga ko aka fara gini kaɗan, amma ba a kammala gine-ginen ba.
An kuma ce ya bar gidaje guda 320 a wasu garuruwa na Najeriya da kuma ƙasashen waje.
Ya bar motoci guda 280 da ake amfani da su, sannan akwai wasu motoci guda 120 da ba a amfani da su, suna ajiye ne kawai.
An ce ya bar hannayen jari (shares) da darajarsu ta haura naira tiriliyan 30 a kamfanoni da ke cikin Najeriya da ƙasashen waje.
A wata hira da ya bayar a shekarar 2022, ya ce ya fara sayen jiragen sama masu zaman kansu tun a shekarar 1967, inda farashin jirgi ɗaya a wancan lokaci ya kai dala 120,000 na Amurka. An ce yana da jiragen sama masu zaman kansu guda 10, kuma darajar kowannensu ba ta gaza naira biliyan 1 ba.
Ya rayu tare da mata huɗu, ya bar 'ya'ya sama da 45 da jikoki sama da 150.
An binne shi a birnin Madina da ke ƙasar Saudiyya, k**ar yadda ya yi wasiyya.
Muna Adu'a Allah Ubangiji yaji kansa da Rahama Ameen 🙏
Allahu Akbar!
08/09/2026
🇮🇷🇺🇸 Iran Ta Kwace Wata Jirgin Ruwa Marar Matuki na Amurka a Mashigin Hormuz.
Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC ta sanar da cewa ta kwace wani babban jirgin binciken ruwa marar matuƙi (UUV/AUV) na Amurka a kusa da mashigar Strait of Hormuz, a wani abin da ta bayyana a matsayin aikin leƙen asiri mai sarkakiya.
Wane irin jirgi ne?
Rahotannin sun bayyana jirgin a matsayin Anduril Dive-LD, wani babban jirgin ruwa mai sarrafa kansa da kamfanin Anduril na Amurka ya ƙera. An ce yana da tsawon kusan mita 5.8, nauyinsa kusan tan 3, kuma yana iya yin ayyuka na tsawon kwanaki tare da nutsewa zuwa zurfin da ya kai kusan mita 6,000.
Irin wannan na'ura ana iya amfani da ita wajen:
leƙen asiri da tattara bayanan ruwa
taswirar ƙarƙashin teku
ayyukan gano nakiyoyi
Da sa ido kan ababen more rayuwa da ke ƙarƙashin ruwa.
IRGC ta ce an gano, an k**a sannan aka kwato na'urar zuwa cikin Iran.
Ta kuma ce za ta fitar da hotuna da bidiyo na na'urar da aka k**a.
Abin lura shi ne cewa hoton da majiyoyin Iran s**a fitar yana da k**anni sosai da samfurin Anduril Dive-LD, kuma wani rahoto na Naval News ya ce wasu ƙananan siffofin na'urar ma sun yi daidai da wannan ƙirar.
Sai dai har yanzu ba a samu tabbacin kai tsaye daga Amurka cewa wannan na'urar mallakin sojin ruwan Amurka ce ba.
Har zuwa yanzu Amurka ba ta tabbatar da cewa Iran ta k**a wannan na'urar ba.
Dr Ayman Muhd Sareena kuyi following kuyi share don samun labarai da Dumi Duminsu.
08/09/2026
Da kasan yanda mutane zasu manta da kai bayan mutuwar ka-da Baka rayu kana neman yardar su ba😩😩😩😩
08/09/2026
YANZU-YANZU: Manyan Kasashen Duniya 12 Sun Sanyawa Kasar Isaraila Takunkumi
Kasashe 12 sun sanar da cewa suna shirin kakaba takunkumin ƙasa, ko kuma su matsa a samar da matakin bai ɗaya na Turai, kan cinikayyar kayayyakin da ake samarwa a matsugunan Isra’ila da ke yankunan Falasɗinawa da aka mamaye, musamman Yammacin Kogin Jordan.
Kasashen sun ce matakin ya biyo bayan ƙaruwa da hare-haren masu matsugunan Isra’ila kan Falasɗinawa da kuma ci gaba da faɗaɗa matsugunan, wanda suke ganin yana ƙara tsananta rikicin yankin.
Daga cikin ƙasashen da s**a bayyana wannan matsayi akwai Birtaniya, Faransa, Kanada, Denmark, Finland, Iceland, Ireland, Norway, Poland, Portugal, Spain da Sweden.
Matakin na ƙara nuna yadda matsin lamba daga wasu ƙasashen Turai ke ƙaruwa kan manufofin Isra’ila a yankunan da aka mamaye, musamman game da faɗaɗa matsugunai da makomar kafa ƙasar Falasɗinu.
08/09/2026
😂 Hhhh Allah yayi muku Albarka 300😳
08/09/2026
🚨🇮🇷🔥SHIN KAI MA HAKA KAKE TUNANI AKAN IRAN??? Idan kana tunanin Iran ba ta da makamin da zai iya isa nesa cikin kankanin lokaci, ka tsaya ka karanta wannan! 🇮🇷🔥
Wannan makamin da kuke gani sunansa “Kheibar Shekan.” Iran sun ƙirƙire shi ne tun a 2022. Tun da s**a ƙirƙire shi, ba su taɓa amfani da shi ba sai da ’ya’yan wahalar can s**a tsokano su tukunna.
Akwai makamin Kheibar Missile bayan wannan Kheibar Shekan ɗin. Kheibar Shekan shi ne babban fitinannen, saboda yana amfani ne da Solid-Fuel.
Yanzu haka Iran suna da wannan makamin kusan guda 2,000 kwance yana barci.
Tazarar tafiyar da ke tsakanin babban birnin Iran, wato Tehran, zuwa naka babban birnin a Nigeria, wato Abuja, kenan, baki ɗaya tazarar kilomita dubu 5 da 300 ce (5,300KM).
Hakan yana nufin idan Iran ta cillo mana Kheibar Shekan zuwa Abuja, within 15 minutes zaka ji labarin duk mutanen Hotoro har sun tsallaka Tal’udu.
That's means, idan ka taso daga Kabuga, tun ma kafin ka zo Gadar Lado, tuni an shafa Fatiya, kowa ya ɗore sabgar gabansa.
Idan ma baka gane ba, ina nufin idan aka harba Kheibar Shekan daga Maiduguri zuwa Lagos, in sha Allahu, idan ka taso daga ƙofar Ruwa, tun ma kafin ka shigo Rijiyar Lemo, tuni Kheibar Shekan ya je Lagos ya koma Maiduguri sau 8.
Saboda haka, ’yan Nigeria, ku ci gaba da karɓar abinci da tabarmi a matsayin cigaban ƙasa.
07/09/2026
Farashin dizal a kasar Amurka ya kai sabon matsayi mafi girma a tarihi, inda lita 3.9, wato galan guda, ta kai dala 5.85, sak**akon tasirin yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.
Bayanan ƙungiyar masu ababen hawa ta Amurka, AAA, sun nuna cewa sabon farashin ya zarce tsohon tarihi da aka samu a watan Yunin 2022 bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
Farashin dizal na iya ƙara tsadar sufuri da samar da kayayyaki, musamman saboda ana amfani da shi wajen sarrafa manyan motoci, motocin haya, jiragen ƙasa da manyan injuna.
Haka kuma, farashin fetur ya kai dala 4.14 kan galan guda, wanda shi ma ya zama mafi tsada da aka taɓa samu a wannan lokaci, gabanin hutun ranar Ma’aikata a Amurka.
Ƙungiyar AAA ta ce rikicin da ke ci gaba da faruwa a mashigar Hormuz ya sanya farashin ɗanyen mai ya kasance a kusa da dala 90 kan ganga guda.
Amfani 30 nayin sadaka duniya da Lahira duba comment section 👇👇
🌙⚠️ ABUBUWA 7 DA YA KAMATA KA NISANTA DA SU KAFIN KA KWANCI YA BACCI 👇👇
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano State Nigeria � Garko Local Government Sareena
Kano
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Dr Ayman muhd Sareena posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.