DAN ADAM AYAR ALLAH

DAN ADAM AYAR ALLAH

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from DAN ADAM AYAR ALLAH, Health/Beauty, Kano.

Kasancewar mun fahimci hikimar da ta sa Allah ya zabi duniyar Earth ta zama bigire na rayuwar Dan Adam,inshaallhu Zuwa bayan mauludi zan kalli halittar Dan Adam ta kowane fanni don mu fahimce shi.

20/11/2025

Ilimin kimiyya da fasaha ilimi ne Wanda sai da shi duniya ke cigaba.

22/03/2025

Brian Tracy yace : " Mutum zai iya koyawa kan sa wata sabuwar dabi'a da za ta kawo masa cigaba a rayuwar sa a tsawon kwana arba'in ".

Tabbbas wannan gaskiya ne,amma ni ko ina ganin ko a cikin kwana talatin zaka iya yiwa kan ka tarbiyyar koyon dabi'ar da za ta kawo maka cigaba a rayuwa,duba da yadda kwanaki talatin na watan azumi su ke koya mana juriya da hakuri wajen kaucewa miyagun halaye.

05/03/2024

Allah shine zahiri kuma shine badini,

Shi yasa Nazartar al'amuran da s**a shafi rayuwa ita ma ibada ce.

18/09/2022

DANGANTAKAR ZUCIYA DA HUTU KO AIKIN WAHALA.

Akwai wata halitta a jikin aljihun sama na dama dake harbawa da sauri,Yana sa zuciya harbawa da sauri har sau (120) a cikin minti daya,sai Allah Mai tsarkin sarauta ya Samar da wata halitta wadda take rage mata gudu ta maida ita ta dinga harbawa Kamar sau sittin zuwa tamanin a cikin minti daya.

Akwai wata halittar kishiyar wannan aikin ta feso wani sinadari Wanda yake Kara karfi da gudu na bugawar zuciya.

Domin haka ne idan mutum Yana cikin halin hutu ko barci ko nutsuwa sai wannan halitta Mai rage gudun zuciya ta zamo itake da rinjaye, don haka sai zuciya ta dinga harbawa a nitse ,Amma idan mutum na aiki na wahala ko gudu ko yayi fushi ko ya tsorata ko tsananin bege ga wani masoyi,sai waccan halittar Mai Kara gudun zuciya ta Zama ita ce take da rinjaye sai zuciya ta dinga harbawa a guje cikin sauri.

Wannan irin sikeli da yake daidaita harbawar zuciya gwargwadon bukata ba mai hannu a cikin sa sai Allah madaukakin sarki.

Allah ya sa mu dace!

17/09/2022

Duk abin da ka samu ilimin say ta hanyar madosanan sani guda biyar : wato (five sense organs) to yana tabbatar maka da samuwar Allah.

29/06/2022
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano