Narbeela glow

Narbeela glow

Share

We are selling atampa., Shaddah., Materia., Mayafai., Makeup and body decoration

23/09/2025

Gwamnatin Jihar Kano ta Tabbatar da Jami’ar Harkokin Noma Ta Tarayya a Kura

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kai ziyarar duba wuraren da ake shirin gina Jami’ar Harkokin Noma ta Tarayya a karamar hukumar Kura.

Amincewa da kafa Jami’ar ya biyo bayan kudirin da Dan Majalisar Dattijai Mai Wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya gabatar a kwanakin baya, da nufin fadada damar samun ilimi da bunkasa bincike a fannin noma a jihar nan.

A yayin ziyarar, Mataimakin Gwamnan ya jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na mara baya ga duk wani shiri da zai baiwa al’ummar jihar nan damar zurfafa ilimi da samar da abinci da ma ayyukan yi ga matasa.

Wuraren da Mataimakin Gwamnan ya ziyarta sun hadar da Babbar Makarantar Sikandiren ‘Yan Mata ta Kwana dake Kura wato GGSS Kura da kuma Cibiyar Hukumar Bunkasa Kogunan Hadejia da Jama’are dake Kura, wanda ake sa-ran a daya daga cikinsu ne za’a gina jami’ar.

A jawabinsa, Shugaban Karamar Hukumar Kura, Alhaji Rabi’u Abubakar Suleiman Babina ya ce makarantar GGSS Kura tana da girma sosai kuma ta cika sharadin da Gwamnatin Tarayya ta shimfida.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Samar da Jami’ar kuma Tsohon Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Shehu Na’allah, ya ce al’ummar yankin na fatan ganin an bar jami’ar a makarantar tare da barin cibiyar Hadejia da Jama’are kamar yadda take, la’akari da dimbin alfanunta ga manoma.

Wakiliyar mu a Ofishin Mataimakin nabila imam ta rawaito cewa a yayin ziyarar, Mataimakin Gwamnan ya gana da ‘yan kungiyar manoman rani a cibiyar ta bunkasa Kogunan Hadejia da Juma’are.

Ya kuma kai ziyara garin Danhassan don duba wurin da ake fatan mayar da makarantar Kwanan ta GGSS Kura.

22/07/2025

Al'umma a fadin duniya na kara Addu'aoi da tofin Allah wadai na fadan Gaza da isra'il

Daga { Abubakar Bashir Adam Yakasai}

Duniya na ci gaba da matsa wa Isra’ila lamba tare da nuna damuwa kan yadda ake gudanar da yakin Gaza, inda Tarayyar Turai da ƙasashe fiye da 25 – ciki har da Birtaniya, Canada da Japan – s**a yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da jefa bama-bamai a Gaza ba tare da la'akari da fararen hula ba.

Kasashen sun bayyana wannan hari a matsayin “marar mutunci”, suna kuma kira da a dakatar da jefa bama-bamai nan take da kuma kare rayukan fararen hula da s**a maƙale cikin rikicin.

Sun bayyana cewa wajibi ne a mutunta dokokin yaƙi da kare hakkin ɗan Adam, tare da buƙatar a samar da hanyar ceto da kai agaji ga waɗanda rikicin ya shafa.

Wannan kira na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun asarar rayuka da dimbin raunuka a tsakanin fararen hula, musamman mata da yara, a sakamakon hare-haren da ake kaiwa a zirin Gaza.

N imam
S radio

22/07/2025

Al'ummar yankin Daneji dake bangaren gidan sarkin kano sun Roki Sarkin Kano Da Ya Gargadi Ahmad Idris Kan Kiwon Dabbobi Masu Haɗari

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da gaggawa ga hukumomi su dauki mataki kan tsohon Akantan Gwamnatin Tarayya, Ahmad Idris, sakamakon korafe-korafen da al’ummar unguwar Daneji s**a shigar dangane da kiwon dabbobi masu haɗari a gidansa.

Al’ummar unguwar sun bayyana damuwa kan wani rahoto da ke nuna cewa wata macijiya da ake zargin yana kiwo ta tsere daga gidan Ahmad Idris, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba da tsoro.

Sarkin ya bayyana cewa, “Idan wani abu ya faru da jama’a saboda wannan sakaci, to lallai za a dora alhakin hakan a kan Ahmad Idris.” Ya bukaci hukumomin tsaro da na muhalli su shiga cikin lamarin nan da nan domin kare rayukan al’umma.

Haka kuma, Sarkin ya shawarci jama’a da su kasance masu lura da duk wani abu da ka iya zama barazana ga lafiyarsu, yana mai jaddada cewa tsaron lafiya da zaman lafiya wajibi ne a kiyaye a kowane lokaci.

N imam
S radio Nigeria

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


No. 9 GTC Quarters Opp Audu Bako Stateroad Kano
Kano