Ibn Ibrahim Abuja'afar

Ibn Ibrahim Abuja'afar

Share

Da'awah

21/09/2024

*NASIHA GA DALIBAI MATA 0011*

*Lallai ki sani cewa* *dukkanin wata shiriya da za ki samu a cikin* *rayuwar ki tana a cikin Al'qur'ani ne da abinda* *Al'qur'ani ya qunsa, don haka kar duk wani karatu da za kiyi ya dauke miki hankali da ba ma wa* *Al'qur'ani lokacin ki, ko* *ya ya ya zamanto kina da wani tsari, duk qanqantar lokaci ki tsara wa kanki cewa lallai kina da wani kaso na Al'qur'ani a cikin rayuwar ki.*

*Domin a cikin shi ne za ki samu waraka na* *abubuwa da da ma,* *wanda kika iya riskarsu ma da wanda baki riska ba*
*Duk wani abu da za ki tattara, duk wani abu da za kiga kin samu na* *cigaba, idan ya zamanto kin raba layi da Al'qur'ani to baza ki samu aminci ba, ko da kuwa kina jin cewa akwai wannan aminci, akwai Inda Allah zai tauye ki ya haramta miki.*

*Don haka ki sa wa kanki rabo na Al'qur'ani, a cikin shi akwai shiriya, a cikin shi akwai waraka, a cikin shi akwai haske, kuma ba sharadi ba ne ba na cewa idan ni 'yar boko ce sai na raba hanya da* *Al'qur'ani sannan boko na zai cika ba Inda aka rubuta wnn sharadin*
*Ba Inda aka ce sai na* *rabu da addini na sannan zan zama 'yar boko, don* *haka kiyi kokari ki kula da wnn*

*Allah ya tsaremana imaninmu Ameen ameen*

17/09/2024

With طلب العلم فريضه – I just got recognised as one of their rising fans! 🎉

30/08/2024

*_IMAM HUSSAIN DA YAZID DAN MU'AWIYA_*

*_TAMBAYA (163)❓_*

_*Assalamualaikum barka da safiya ya aiki Dan Allah menene a tsakanin imam Hussain da Yazid Dan Mu awiya kwanan Nan abun da yake ta trending kenan wasu na bayan imam Hussain wasu na bayan Yazidu menene gaskyar lamarin*_

*_AMSA❗_*

*_Waalaikumus salam Warahmatullahi Wabarakatuhu_*

*_Dukkansu bayin Allah ne wadanda Allah ya yarda dasu_*

*_Tarihin abinda ya faru tsakaninsu yana da tsayi kamar yanda na karanta a cikin Mukhtasar Minhajus Sunnah📗 na Ibn Taimiyya Rahimahullah_*

*_Matsala ce ta shugaban ci👑 ta shiga tsakanin su, bankado matsalar bashida faida ga musulmi😔_*

*_Muawiya Ibn Abu Sufyan ya kasance Sahabin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ne wanda daga baya ya zamo gwamna a garin Sham (Syria a yau) a zamanin khalifancin Sayyadina Umar da Uthman (Radiyallahu anhuma)_*

*_Shine ya zamo khalifan Umayyad na farko (661-680 CE) bayan rasuwar Sayyadina Ali Ibn Abi Talib, khalifa na 4_*

*_Sayyadina Yazidu Kuma, Dan Mu'awiya ne, Wanda ya zamo khalifan Umayyad bayan rasuwar Mu'awiya (680 - 683 CE)_*

*_Fadan⚔️ dake tsakanin Mu'awiya da Hussain ya samo asali ne silar sahalewar da Mu'awiya yayiwa dansa akan ya gajeshi a Khilafanci Wanda hakan ya saba da ala'adar Khilafa a addini (Wanda sai Committee din Shurah sun saka hannu). Wadanda s**a yi bore sun hada da jikan Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam wato Hussain Ibn Ali. Shi Kuma yayansa Hassan shine ya sasanta fadan shiyasa Yan Shi'a S**a tsaneshi, zakaji sunfi ambaton ya Hussain akan ya Hassan🤔_*

*_Hussain Yana ganin bai kamata a dora Yazid a matsayin magajin Mu'awiya ba saboda hakan ya ci karo da tsarin addini. Wannan rigimar ta cikin gida itace ta zama silar yaqin Karbala a shekarar 680 Miladiyya Wanda ananne yan Shi'a s**a kashe Hussain🥹_*

*_Kamar yanda kasan ilimin Masdalahul Hadith to Haka shima Ilimin "Masdalahul Tarih" wato yanda ake tace tarihi, shine ya zama silar da yan Shi'a suke ta Zagin abokan fiyayyen halitta 😳(Sallallahu alaihi wasallam). Yanzu don Allaah zaka so mutum ya dinga Zagin abokan mahaifinka🤢. To Ina Kuma ga Wanda zai zagi Sayyadina Abubakar, Umar da Uthman😭ya fifita Sayyadina Ali da Hussain_*

*_Ki karanta karatun Marigayi Shaikh Albany Zariya mai taken: "Hiqbatun Minat Tarikh" muqaddimar: "Tasdidul Isaba Fi Ma Shajara Bainas Sahaba" wallafar al-allamatil Shaikh Ziyab Ibn Sahad Ali Hamdan al-Ghamidi, anan zakiga yanda ake tantance tarihi kamar yanda ake tace zuma farar saqa🐝_*

*_Yan Shi'a sun baude daga tafarkin Sunnah😭 sun rarrabu alhalin Allaah Azzawajallah yace kada ku rarrabe🙅‍♂️_*

( وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ تَفَرَّقُوا وَاخْتَلَفُوا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْبَيِّنَاتُ ۚ وَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ )

آل عمران (105) Aal-Imran

*_Kuma kada ku kasance kamar waɗanda s**a rarrabu kuma s**a sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma._*

*_Ko dayake ma su fa basu yarda da wannan Qur'anin da mu musulmai muke amfani dashi ba suna claiming ai an caccanzashi🤦🏼‍♂️. Ko ya zasuyi da ayar da Allaah yace Shi ya saukarda littafin Kuma zai Kare abinSa🤔_*

( إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ )

الحجر (9) Al-Hijr

_*Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.*_

*_Allaah yace kada mu zamo ƙungiya ƙungiya_*

( مِنَ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ )

الروم (32) Ar-Room

_*Wãtau waɗanda s**a rarrabe addininsu kuma s**a kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.*_

*_Amman saboda sakarcin Shi'ah da Jahilci da biyewa son zuciya sai suke ma Kiran Kansu da ƙungiya din gaba daya (Wato Shi'ah)_*

*_Da akwai wani Malami Dan Shi'a Mai suna Shaikh Ali Khalil Ankantara Wanda gaba daya baya jin qishin ruwa💦 saidai yasha don marmari. Hakan ta faru a gaske silar mafarkin da yayi anyi tashin ALQIYAMA_*

*_Gashinan a tafkin ruwan Alkauthar 😍tareda Ma'aiki da Sahabbansa, sai ya tafi wajen Sayyadina Ali saboda bayason sauran Sahabban. Sayyadina Ali ya kauda kansa✋ yaqi kulashi, can sai Ma'aiki ya kirashi, yace masa Zan shayar dakai ruwan Alkauthar amman kayimin alqawarin zaka dinga son Sahabbaina gaba daya. Nan take ya dauki alqwarin, Ma'aiki ya shayar dashi ruwan💦. Nan take ya farka daga baccin a tsorace😳_*

*_Daganan ya watsar da baqaqen kayannan nashi yacewa dalibansa da dubunnan mabiyansa su gaggauta barin Shi'ah babu alkhairi ko kadan a cikinta. Daganan ya riqe Sunnah gamgam. Tun daga mafarkin nan da Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam ya shayardashi ruwan Alkauthar, iyalansa s**ace bai qara jin kishin ruwa ba. Allaahu Akbar !_*
*_Sahabbai ba maasumai baneba don sun fada cikin hadisin: Dukkan Yan Adam masu laifi ne saidai mafi alkhairinsu sune masu yawan tuba🤷‍♂️_*

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «كلُّ بني آدم خَطَّاءٌ، وخيرُ الخَطَّائِينَ التوابون».
[
رواه الترمذي (2499)، وحسنه الألباني، فهنا لم يتم استثناء أحد

*_Allaah yace_*

( يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ )

المؤمنون (51) Al-Muminoon

_*Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.*_

( وَإِنَّ هَٰذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاتَّقُونِ )

المؤمنون (52) Al-Muminoon

_*Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.*_

( فَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ زُبُرًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ )

المؤمنون (53) Al-Muminoon

_*Sai (al'ummar) s**a yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.*_

_*Son sahabbai wajibine saboda Allaah ya yarda dasu💞. Shaidan ne yake QOQARIN ya jefa mana qiyayyarsu a xuqatanmu kamar yanda ya jefawa Yan Shia tsanar su*_

_*Abinda yafi shine ka roqa musu Rahamar Allah 🤲sannan ka qyale abinda ya faru tunda ya riga da ya faru*_

_*Wallahu taala a'alam✒️*_

_Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk_

*_Amsawa:_*

*_Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)_*

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

whatsapp.com

30/08/2024

MATARKA SARAUNIYARKA.
-
❝Ka riƙi matarka a cikin gidanka tamkar wata sarauniya, kada ka maisheta tamkar wata baiwa a cikin gidanka wacce ba ta da wani amfani a wajenka face sai dai ta biya maka buƙatarka a lokacin da ka buƙaceta. Kubi salo na jin daɗin soyayya a zamantakewar aurenku, ku haifarma da kanku farin ciki mai ɗorewa a tsakanin ku, kada wani sashe ya muzgunawa wani sashe a tsakaninku. Ku mutumta juna, ku ɗebe ma junanku kewa, hakan shi ne zai sa kuji daɗin aurenku ta re❞
-
"Wasu mazan s**an nuna maƙurar soyayyarsu ga ƴan matansu kafin su aure su, amma da zarar anyi auren an ɗauki tsawon lokaci sai kaga wannan soyayyar ta ragu ba tare da matan sunyi musu laifin komai ba"
-
"Zaiyi matuƙar wahala kaga mace tana matuƙar son ka kafin kuyi aure, bayan auren kuma ta daina nuna maka soyayya, sai dai idan kaine ka fara nuna mata hakan. Mata s**an ririta mazajen su a gidan auren su fiye da yadda mazan suke nuna ta su soyayyar ga matayen su"

Abu~Ja'afar...

06/06/2024
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Karu?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Mararaba Federal Capital Territory Abuja
Karu
ABUJA'AFAR

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibn Ibrahim Abuja'afar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Karu.