Authentic Hausa media
This page is for Hausa all round news
08/01/2026
Majalisar Dokokin jihar Rivers ta sake ƙaddamar da yunƙurin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa bisa zargin aikata manyan laifuka.
Yayin wani zaman gaggawa da ta yi a ranar Alhamis, majalisar ta ce Fubara ya kashe kuɗaɗe ba tare da amincewarta ba da kuma rushe ginin majalisar.
08/01/2026
Iran Na Shirin Kafa Sabon Tarihi: Iran na ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa (Shaheed) guda 400 a kowace rana, a halin yanzu tana da kimanin jirage marasa matuƙa 80,000 a sahun gaba masu shirin shiga fagen daga.
Nan da Karshen Wannan wata adadin jiragen Yakin Shasheed zai haura zuwa dubu 165,500.
Hasashe ya nuna cewa Iran zata zama ƙasar da ta fi kowacce yawan masu sarrafa jiragen yaƙi marasa matuƙa a duniya. Wannan aiki ya gudana ne da taimakon kasar Rasha.
Allah Ya karawa Annabi Daraja
Kuyi Following din shafin GM HAUSA NEWs
08/01/2026
📌 Wannan bala’i Kenan 😌
Ana kiranshi mouth ulcer ko Kuma canker sore.
Nakirashi da bala’i neh saboda duk wadda wannan abun ya taba fita mishi yasan yadda abun yake uzzurawa mutum.
Ciwon fatar harshe raunuka ne masu zafi a harshe da ke sa cin abinci, magana, ko hadiya abu ya zama da wahala.
Yawanci ba cuta mai hatsari ba ce, kuma tana warkewa da kanta, amma kulawa mai kyau na rage zafi da saurin warkewa.
📌 Dalilin samunsa ya hada da
✅Cizon harshe da gangan ko cikin kuskure,
✅hakora masu kaifi ko braces,
✅karancin sinadaran jiki (iron, vitamin B12, folic acid),
✅damuwa da rashin barci,
✅kamuwa da kwayoyin cuta,
✅Da cin abinci mai yaji, zafi ko tsami.
Nasan zaku so kuji yadda Zaku magance shi
Toh duba comment section 👇 👇 👇 👇 👇
Write by..
Bilal Yakubu Ballah
06/01/2026
08/01/2026
Anyi yunƙurin kashe shugaba Traore na Burkina Faso.
Gwamnatin ƙasar Burkina faso tace ta daƙile wani shiri na kashe shugaban ƙasar Ibrahim traore da akayi.
Ministan tsaro Mahamadou Sana, yace tsohon shugaban ƙasar, Paul Henri Damiba, wanda Traore ya hamɓarar a shekarar 2022 shi ne ya kitsa wan nan hari da taimakon Ƙasar Ivory Coast
07/01/2026
03/01/2026
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ja ragamar gwamnatin Venezuela har zuwa lokacin da al'amura za su daidaita tare da miƙa mulki ga gwamnatin da za a kafa.
Kawo yanzu dai bayanai na cewa Mista Maduro na New York inda zai fuskanci shari'a kan zargen-zargen safarar miyagun ƙwayoyi.
Karin bayani - https://bbc.in/4pnamsu
03/01/2026
Wannan Itace "Kim Ju-Ae" Ƴa ɗaya tilo ga Kim Jong-Un Shugaban kasar Korea Ta Arewa 😍 Wannan Yarinyar Itace Yarinya Wacce Tafi Kowacce Yarinya Capacity a Duniya 😍 Ance hatta kayen da take sakawa dokane a kasar Korea wata ta saka irin su. Idan ta saka kuwa Hukuncin kisa ne kawai🤣
Har yanzu ba a samu Namijin Daya Taɓa Ƙoƙarin cewa yana sonta ba. Kuna Ganin Dan wacce kasa zai iya daukar wannan kasadar
Daga Jawad Jibrin
03/01/2026
Sojojin Nijeriya sun gano babban Wanda ya tsara harin b@m a masallacin Maiduguri
An gano wanda ake zargi ne bayan wani aikin tsaro na musamman da aka gudanar bisa bayanan sirri a ranar 31 ga Disamba, 2025, a yankin Kalmari na Maiduguri.
A yayin wannan samame da bincike, jami’an tsaro sun k**a mutane 14 da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan harin b@m na kunar b@kin wake.
Allah Ya Kara tona masu asiri
01/01/2026
WATA SABUWA:Wani Babban Malamin Addinin Musulunci Yana Zawarcina, Idan Bai Daina Bibiyata Ba Zan Tona Masa Asiri!
~Aisha Buhari.
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, ta bayyana wani lamari mai tayar da kura, inda ta ce wani babban malamin addinin Musulunci na bibiyarta tare da neman kusanci da ita ba tare da yardarta ba.
A’isha Buhari ta bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ta nuna ɓacin ranta da gargaɗi mai tsanani ga malamin, tana mai cewa idan har bai daina bibiyarta da nemanta ba, za ta fito fili ta tona masa asirin da ya ɓoye.
Ta ce tana mamakin yadda mutumin da ake kallonsa a matsayin abin koyi da jagora a addini zai rika aikata irin wannan ɗabi’a, alhali ana tsammanin ya kasance yana koyar da tarbiyya da tsoron Allah.
“Na yi shiru na dade, amma idan har bai daina wannan bibiyar ba, zan fito na faɗi duk abin da na sani a kansa,” in ji A’isha Buhari.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Maiduguri