Cmrd. Sani b. Yusuf

Cmrd. Sani b. Yusuf

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Cmrd. Sani b. Yusuf, Health/Beauty, G.r.a., Maiduguri.

25/09/2022

DAMAR SAMUN AIKI A GIDAN TALABIJIN:

1. Masu gabatar da Shirye-Shirye
2. Masu karanta labarai
3. Masu dauko rahoto

CANCANTA:
°NCE, OND, Degree, MSc ko makamancin haka
°Iya Fassara turancin zuwa harshen Hausa
°Iya karatu da rubutu da harshen Hausa
°Aika bidiyon minti d'aya a WhatsApp lamba +971 58 504 6632
na aikin da kake nema da takardun neman aiki zuwa: [email protected]
Kafin 15 ga watan Oktoba, 2022

Photos from Cmrd. Sani b. Yusuf's post 22/09/2022

YANZU-YANZU: El-Rufaì ya nada Zaìlanì Gwamnan rìƙon kwarya, ya mìƙa masa Gwamnatì

Gwamna Nasìr El-Rufaì ya mìƙawa Kakakìn majalisar dokokì jihar Kaduna RT Hon. Yusuf Zaìlanì mulkìn jihar Kaduna na wucìn gadì

Gwamnan ya naɗa Kakakin Majalisar a matsayìn muƙaddashin Gwamna ne saboda zaì yì wata tafiya ya bar ƙasar tsawon mako Biyu kuma gashì mataimakiyar Gwamna ma bata ƙasar.

Me zaku ce?

Da Ɗumi-Dumi: IGP Usman Baba Ya Gana Da Manyan Jami'an Yan Sanda a Abuja 22/09/2022

Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Alƙali Baba, ya shiga ganawa da manyan jami'an hukumar yan sanda na faɗin Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa zasu tattauna kan zaɓen 2023, da kuma karuwar cin mutuncin 'yan sanda a bakin aiki da sauran batutuwa.

Da Ɗumi-Dumi: IGP Usman Baba Ya Gana Da Manyan Jami'an Yan Sanda a Abuja Shugaban rundunar 'yan sanda na ƙasa, IGP Usman Alƙali Baba, ya gana da AIGs, DIGs da kwamishinonin 'yan sanda na jihohi 36 da birnin tarayya Abuja kan batutuwa

Kungiyar ‘yan China da ke Kano ta goyi bayan a yi wa makashin Ummita hukunci bisa doka - DCL Hausa 22/09/2022

Kungiyar ‘yan China da ke Kano ta goyi bayan a yi wa makashin Ummita hukunci bisa doka

Karin bayani: https://bit.ly/3BuGjrZ

Kungiyar ‘yan China da ke Kano ta goyi bayan a yi wa makashin Ummita hukunci bisa doka - DCL Hausa Kungiyar ‘yan kasar China da ke kasuwanci a Kano ta yi Allah wadai da kisan da ake zargin wani dan kasar China ya yi wa matashiyar nan Ummita. A cikin wata wasika da Mr. Mike Zhang mai rike da sarautar Wakilin Mutanen China a Kano ya fitar a Litinin din nan, kungiyar ta ce tana

Zan samar da zaman lafiya da Ha’din Kan kasa zan Kuma dawo da imanin a zukatan Nageriya ~inji Peter Obi. 22/09/2022

Zan samar da zaman lafiya da Ha’din Kan kasa zan Kuma dawo da imanin a zukatan Nageriya ~inji Peter Obi.

Zan samar da zaman lafiya da Ha’din Kan kasa zan Kuma dawo da imanin a zukatan Nageriya ~inji Peter Obi. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Mista Peter Obi, ya bayyana cewa zai tabbatar da dorewar zaman lafiya ta hanyar hada kan kasar nan tare da sake gina zamantakewarta da aminc…

2023: Na rantse da Allah za’ayi zaben gaskiya Kuma zan sauka a mulki cike da Gaskiya da adalci ~Cewar Shugaba Buhari a majalisar dinkin duniya. 21/09/2022

2023: Na rantse da Allah za’ayi zaben gaskiya Kuma zan sauka a mulki cike da Gaskiya da adalci ~Cewar Shugaba Buhari a majalisar dinkin duniya.

2023: Na rantse da Allah za’ayi zaben gaskiya Kuma zan sauka a mulki cike da Gaskiya da adalci ~Cewar Shugaba Buhari a majalisar dinkin duniya. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya yi alkawarin barin gadon mulki na gaskiya da adalci yayin da wa’adinsa na shekaru takwas ke kawo karshe a watan Mayun 2023. Shugaban ya ba…

21/09/2022

SHIN: Haryanzu kana cigaba da karbar Albashinka na tsarin N-power ko Kai ma kana cigaba da Jira ta fashe?

21/09/2022

YANZU-YANZU: Ganì Ga Wane.…

Wata budurwa ta mìƙa kanta ga hukumar ƴan sanda a Kano bayan da wanì saurayìn ta ɗan ƙasar Turkìyya ke neman ta ruwa a Jallo

Daga- Nasiru Salisu Zango

Bacci Zai Dunga Yi A Ofis: Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Ya Yi Shagube Ga Tinubu 21/09/2022

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali, ya yi gargadi cewa dan takarar APC, Bola Tinubu zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’ idan aka zabe shi a 2023.

Alkali ya gargadi masu kada kuri’u da su tabbatar da ganin cewa basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Bacci Zai Dunga Yi A Ofis: Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Ya Yi Shagube Ga Tinubu Shugaban jam'iyyar Kwankwaso mai kayan marmari, Rufai Ahmed Alkali, ya cedan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu,likimo zai dunga yi idan ya lashe zabe.

Bashin da ake bin Najeriya ya kai naira biliyan 42.8 a karkashin jagorancin shugaba Buhari - Hutudole 21/09/2022

Bashin da ake bin Najeriya ya kai naira triliyan 42.8 a karkashin jagorancin shugaba Buhari
http://ow.ly/oWx230sreXC

Bashin da ake bin Najeriya ya kai naira biliyan 42.8 a karkashin jagorancin shugaba Buhari - Hutudole Bashin da ake bin Najeriya ya kai naira biliyan 42.8 a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari yayin da kasa ke cigaba da fama da matsalar tattalin arziki. Ofishin dake lura da bashin Najeriya ne ya bayyana a ranar litinin, inda s**a wallafa a shafinsu cewa daga watan Maris zuwa watan yuni ne....

21/09/2022

Ka Da Ku Sake Ku Yi Kuskuren Tare Titin Hanyar Kaduna Zuwa Abuja, Gargaɗin El-Rufa’i Ga Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i, ya gargaɗi ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NASS da ka da su yi kuskuren tare kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Jaridar IDON MIKIYA ta ruwaito cewar, gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Talata, biyo bayan kira da shugaban ƙungiyar ɗalibai NASS reshen jihar Kaduna Dominic Philip, ya yi na tare titin hanyar Kaduna zuwa Abuja, sakamakon yajin aikin da ya ƙi ci - ya ƙi cinyewa da ƙungiyar Malaman jami'o'i ta ƙasa ASUU ke yi.

Dominic Philip, a cikin wata sanarwa, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su rufe babban hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Laraba, don matsawa gwamnati wajen ganin an kawo ƙarshen yajin aikin.

Daliban jami’o’in gwamnati a Nijeriya dai na gudanar da zanga-zanga a wurare mabanbanta a ƙoƙarin su na tursasawa gwamnati ta biya buƙatar ASUU domin kawo ƙarshen yajin aikin da s**a shafe watanni shida suna yi.

Daliban a ranar Litinin ɗin da ta gabata a jihar Legas sun toshe hanyoyin zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), inda s**a hana zirga-zirga a hanyar na tsawon sa’o’i.

©Idon Mikiya

21/09/2022

YANZU-YANZU: Kungiyar Malaman Jami’o’i Nigeria ASUU, Tayi Watsi Da Umarnin Da Kotu Tayi Musu

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Kungiyar malaman Jami'o'in Nigeria ASUU ta bayyana cewa, kotu baza ta iya tilasta wa malaman jami’o’i su koma bakin aiki ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a yayin da kotun kolin masana’antu ta kasa ta bayar da umarnin, a yau laraba

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Telephone

Website

Address


G.r.a.
Maiduguri