Raudatul haq Islamic medicine and research

Raudatul haq Islamic medicine and research

Share

Ruqyah Sunnah | Islamic medicine
✨ Maganin Sihiri • Kambu baka • medicine
🩺 Duba Mara Lafiya & Shawara Ta Gaskiya
🤲 Waraka Daga Allah Kadai

18/05/2026

PART (1) MENENE KAMBUM BAKA, BAMBAMI TSAKANIN KAMBUM BAKA DA MAITA....yanda kambum baka yakeda tasiri....

KanbunBaka

14/05/2026

Part two(2) cigaba da bayani gameda manya manyan bambance bambance tsakanin sihiri da shafar Aljani dakuma sharrin bokaye da yanda suke yaudarar mutane.....

ShafarAljani

13/05/2026

Manya manyan bambance bambance tsakanin sihiri da shafar Aljani dakuma dangantakar tsakanin bokaye da yanda suke dabarun nasu.....

13/05/2026

‎MAHIMMANCI (MAGARYA) DA MAGUNGUNANTA A MUSULUNCI........

‎ Itadai Itaciyar Magarya (Sidr) tana daga cikin muhimman bishiyoyi da s**a shahara tun fil-azal, musamman a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, Bishiya ce mai ganye masu sheki da yaya masu dandano, wadda take da matsayi mai girma a Musulunci, al’adun Larabawa, da kuma fannin magungunan na Musulunci (Islamic Medicine).

‎Allah Madaukakin Sarki ya ambaci Magarya a cikin Alqur’ani Mai Girma, Haka Manzon Allah (SAW) yayi ishara da ita Acikin Hadisai, hakan ne yake nuna girmanta da darajarta a addinin Musulunci.

‎MAGARYA A AL-QURANI DA SUNNA.

‎An ambaci bishiyar Sidratul-Muntaha a daren Isra’i da Mi’iraji, wadda take wata babbar bishiyar magarya a saman sammai. Wannan yakara nuna matsayinta, Haka Acikin Hadisi ingantacce da Imam ya ruwaito, Manzon Allah ya ce:
‎“Ku wanke mamaci da ruwa da ganyen Sidr (magarya).”

‎Haka kuma Annabi ya umarci Sahabbai da amfani da magarya wajen: Tsarkake jiki, Kawar daciwon ido, Kare mutum daga cututtukan ruhi,haka akwai Magarya ta Zuma (Sidr Honey), Daya daga cikin manyan falalar bishiyar magarya shi ne Kudan zuma na yin kiwo a kan furanninta Suna samar da Zumar Sidr, wadda take Daya daga cikin zumomin daji mafi tsada a duniya, Mai dauke da antioxidants, Mai karfafa garkuwar jiki, haka kuma tana magance cututtukan ciki, hanta, da rigakafi ga cutar daji.

‎NAU'OIN YAYAN MAGARYA.
‎‘Ya’yan magarya sun bambanta ta, Girma
‎Launi, Dandano, Siffa, Akwai Nau’in da ake kira “Apple Sidr” saboda suna k**a da apple, sai Nau’in da ake kira “Zaitun Sidr" saboda k**anninsu daya da zaitun, haka akawai Sauran nau’o’i ta da dama masu kamshi da dandano mai dadi.

‎AMFANIN MAGANAR A MUSULUNCI (DAKI-DAKI).
‎Ganye magarya yana Tsarkake Jiki da Ruhi, haka Ana amfani da ganyen magarya wajen, Wanke mamaci, Tsarkake jiki daga kazanta, Rage saurin lalacewar gawa, Maganin Cututtukan Ruhi,
‎Magarya nada tasiri wajen Karya sihiri,
‎Kawar da kambun baka, Maganin cutar shaidanu, Cutarwar ido (ain), Ganyen magarya na Tsarkake jini da hanji,
‎Rage cholesterol mai cutarwa, Maganin ciwon makogwaro da (trachea), Taimakawa wajen gyaran kashin daya karye, Rage zafin jiki, Kwalliya ga Fata,
‎Ana amfani da ganyen magarya wajen
‎Rini ko cenza launin gemu ko fata,Kara sheki da lafiyar fata, Tsabtace fata daga kazanta, guraje, tana saka Gashi yayi Kyau, Magarya na Kara tsawon gashi, Kara sheki, Hana zubar gashi, Kara karfi da lafiyar gashi, Magarya na Maganganun da dama k**ar yadda manya likitocin musulunci s**a fada.

‎Magarya Maganine ga jiki da ruhi,
‎Hujja ce daga Alqur’ani da Sunnah
‎Hanya ce ta kariya daga cututtuka na zahiri da na boye.

‎Amfani da magarya tare da imani,da yakini da bin koyarwar Annabi na daga cikin hanyoyin samun cikakkiyar lafiya

‎ABDUSSAMAD ADAM FUNTUA
‎Director
‎Raudatul Haq Islamic Medicine & Research Center
‎📞 08033319466







13/05/2026

‎AMFANIN (SENNA MAKKI) DA MAGANINTA A MUSULUNCI...........

‎Itadai Senna Makki itaciya ce mai dumbin tarihi da amfani a fannin Tibbun-Nabawi, Ana samunta a kasashe da dama k**ar Masar, Pakistan, da yankunan Larabawa, musamman yankin Hijaz.
‎Ana danganta ta da Makki ne saboda a Makkan ake samun mafi ingancin Senna, kuma manyan malamai da likitocin Musulunci sun jaddada muhimmancint Fitattun malaman Tibbu k**ar Ibnul Qayyim ya bayyana cewa Senna Makki tana daga cikin mafi ingancin ganyayyakin magani, kuma tana da matukar amfani idan aka yi amfani da ita bisa ka’ida.

‎DALILIN AMFANI DAGA SUNNA NA
‎Annabi Muhamma(SAW) yayi wasiyya cewa, “Ku yi amfani da Senna da Sannut, domin suna warkar da kowace cuta, sai Samm.” Sai aka tambaya: “Ya Manzon Allah, menene Samm?” Sai ya ce “Mutuwa.” (Ibn Majah ya rawaitoshi, Albani ya inganta shi).
‎Wannan Hadisi yana nuna darajar Senna Makki a Musulunci a matsayin magani mai albarka.

‎ haka Ibnul Qayyim (ya bayyana a cikin littafinsa Tibbun-Nabawi cewa Senna tana da nau’i biyu: doguwa da gajera
‎Mafi ingancinta ita ce ta Hijaz, musamman ta Makka Magani ce mai ƙarfi, mai tsarkake jiki, kuma mai kariya daga cututtuka da dama.

‎AMFANIN (SENNA MAKKI) DAKI-DAKI

‎Senna Makki ganye ne mai dauke da fa’idodi masu yawa ga lafiyar jiki, daga ciki Akwai: Tsarkake Hanji, Tana wanke hanji
‎Tana kawar da datti, guba, da abubuwan da ke haddasa cuta Acikin hanji, haka za'a iya amfani da ita kafin wasu gwaje-gwajen likita na zamani, k**ar colonoscopy. Maganin Matsalolin Mata, Rage ciwon mara, Taimakawa wajen zubar jini mai yawa na haila ko bayan haihuwa, Rage radadin jinin al’ada, Laxative na Halitta,
‎Tana taimakawa wajen motsa hanji,
‎Maganin kumburin ciki (constipation) Rage Gajiya da Radadin Jiki, Tana taimakawa wajen rage gajiya,
‎Rage wasu ciwukan gabbai dana jiki, Maganin Sihiri (da izinin Allah),
‎A fahimtar malamai da masana Ruqya, tana taimakawa wajen tsarkake jiki daga
‎tasirin sihiri.

‎(SANNNE) GAME DA RAGE NAUYI (KIBA) (WEIGHT LOSS).
‎Wasu likitocin Musulunci na ganin Senna Makki na iya taimakawa wajen:
‎Rage kumburin jiki, Rage kitse Amma na wucin gadi, Amma babu cikakkiyar hujjar kimiyya data tabbatar dashi matsayin maganin rage nauyi kai tsaye. Saidaima wasu manyan likitocin musulunci kamrsu Razi, ibn sina, suna ganin Yawan amfani da ita na iya jawo: Gudawa mai tsanani
‎Asarar ruwa a jiki, Raunin jiki.

‎ILLAR AMFANI DA (SENNA) BA TARE DA KA’IDA BA.
‎ Ba a yarda a yi amfani da Senna Makki:
‎Na dogon lokaci ba, Ko ba tare da shawarar masani ba Illolinta sun hada da:
‎Ciwon ciki, Tashin zuciya, Gudawa mai tsanani. kasaka mai tsanani.

‎ FADAKARWA MAI MUHIMMANCI GAME DA (SANNA MAKKI.
‎Ka tabbata ka tuntubi masani kafin amfani da Senna Makki, domin rashin sanin yadda ake amfani da ita na iya haifar da matsala ga lafiyar jiki.
‎Maganine mai amfani Amma idan aka yi amfani da shi ba daidai ba, na iya zama illa.

‎ABDUSSAMAD ADAM FUNTUA
‎Director, Raudatul Haq Islamic Medicine & Research Center
‎📞 08033319466





13/05/2026



‎SIRRIN MAGANI A MUSULUNCI, ABIN DA KIMIYYA TA GANO, ANNABI MUHAMMADU (SAW) YA RIGA YA FAƊA..........

‎Mu’ujizojin Kimiyya a Fannin Magani
‎Musulunci yana karfafa neman magani, kuma yahana yin sakaci da lafiya, Neman magani bai saba da tawakkali (dogaro ga Allah) ba, Abinda aka haramta kawai shine yin magani da abinda Allah Ya haramta, saidai idan larura ta tilasta hakan.

‎MAGANI A MUSULUNCI (Medicine in Islam).
‎Akwai tambayoyi da yawa game da maganin Musulunci:
‎Shin ilimin likitanci ne kawai?
‎Ko maganin da Musulmi s**a yi amfani da shi a tarihi?
‎Ko kuwa tsarin magani ne da aka gina bisa Alqur’ani da Sunnah?
‎Gaskiyar magana ita ce:
‎Maganin Musulunci cikakken tsari ne da ke tafiya tare da koyarwar Ubangiji.
‎Manyan ginshikin Magani a Musulunci sun hada da:
‎1. Bin koyarwar Musulunci da kyawawan ɗabi’u.
‎2. Amfani da hankali da ilimi a aikin magani, da jinyar mara lafiya.
‎3.Kula da jiki, hankali da ruhi (holistic approach).
‎4. Tsari na bai daya dake amfanar da kowa (universal approach).

‎ TANTANCE CUTA DA TAWAKKALI
‎Addinin musulunci yanuna muhimmiyar ka’ida ta magani, wato: Dole ne a fara gano cuta daidai (diagnosis), ta hannun kwararru, sannan a rubuta maganin da yadace. saidai Warkewa tana samuwa ne da izinin Allah, Da Amfani da Ilimi wajan gano cuta, haka Da bada maganin daya dace Da ka'idar musulunci.

‎Neman magani bai saba da tawakkali ba, k**ar yadda: Cin abinci da shan ruwa bai sabawa tawakkali, bal ma wajibine, haka Gujewa abinda zai jawo cuta ko mutuwa bai sabawa tawakkali, saidai kin hakan sabawa Allah ne, dominma yin addu’a don samun lafiya ibada ne.
‎ Musulunci bai hana magani ba, Ya tsara magani ne, Ya hada addini, kimiyya da lafiyar dan Adam.

‎ABDUSSAMAD ADAM FUNTUA
‎Director, Raudatul Haq Islamic Medicine & Research Center
‎📞 08033319466

‎MaganiAMusulunci








13/05/2026

DABINO ABINCI JIKI DA RUHI, TASIRIN KWAKWALWA DA HANKALI.........

‎Dabino a cikin Alqur’ani Mai Girma
‎Allah Madaukakin Sarki ya ambaci dabino a wurare da dama a cikin Alqur’ani, yana nuna girman darajarsa da albarkarsa. Allah yace: “Daga dabino da inabi kuna samun Abin sha da kuma abinci mai kyau.” (Suratu An-Nahl: 67).
‎Wannan aya na nuna cewa dabino abinci ne mai alheri, gina jiki, kuma mai albarka. Dabino ga Mata Masu Juna Biyu, Allah ya umarci Maryam (AS) dataci dabino a lokacin haihuwa: “Ki girgiza jikin itacen dabino, zai saukar miki da sabbin dabino.” (Suratu Maryam: 25). Malamai sun bayyana cewa wannan hujja ce da ke nuna: Dabino yana saukaka haihuwa
‎Yanaba jiki Karfi da kuzari, Yana taimakawa wajen dawo da ƙarfin jiki bayan haihuwa.

‎DABINO A CIKIN HADISIN ANNABI (SAW)
‎Dabino kariya ne daga cuta, Annabi Muhammad (SAW) yace: “Wanda yaci dabino bakwai na Ajwah da safe, ba sihiri ko guba da za su cutar da shi a wannan rana.” (Bukhari da Muslim). Wannan hadisi na nuna cewa dabino, musamman Ajwah, yana da tasiri da kariya ga jiki. Dabino abinci ne mai wadatar jiki Annabi (SAW) ya ce: “Gidan da babu dabino a cikinsa, mutanen gidan suna fama da yunwa.” (Muslim ya ruwaitoshi). Wannan yana nuna cewa dabino cikakken abinci,
‎ Bude baki da dabino Sunnah ce, Annabi Muhammad (SAW) ya kasance yana bude baki da dabino: “Idan dayaku zai yi buda-baki, yayi da dabino.”(Abu Dawud ya ruwaitoshi). Dalili kuwa shine:
‎Dabino yana mayar da kuzari cikin gaggawa, Yana da saukin narkar da Abinci bayan azumi.

‎MAGANGANUN MANYAN MALAMAI DA LIKITOCIN MUSULUNCI GAME DA DABINO.
‎Ibn Qayyim (RA) Acikin Zadul Ma‘ad yace:
‎“Dabino yana karfafa ciki, yana tsabtace hanji, yana kara jini.” Ibn Sina (Avicenna)
‎A cikin Al-Qanun fi Ṭ-Ṭibb yace: “Dabino yana kara kuzari, yana gyara jiki, yana taimakawa koda, zuciya da jijiyoyin jiki.”
‎Imam Al-Dhahabi, Ya bayyana cewa: “Dabino na daga cikin abincin da ke kara lafiyar zuciya.” Sheikh Ibn Baz (RA),
‎Yace: “Cin dabino Sunnah ce kuma yana da Amfani ga lafiya bisa koyarwar Annabi (SAW).” Haka kuma, manyan malaman Ruqyah da likitocin Musulunci, suna jaddada cewa dabino: Yana karfafa jini
‎Yana taimakawa wajen magance sihiri da hassada (musamman Ajwah). Yana karfafa kwakwalwa da zuciya Yana magance raunin jiki da gajiya, Wannan duk ya dace da abin da kimiyya ta gano a yau.

‎DABINO ABINCINE – MAGANINE– SUNNAH NE –NI'IMACE DAGA ALLAH.
‎Dabino yayan itace ne mai cike da sinadarai masu gina jiki. Yana da fa’idodi masu yawa ga lafiyar jiki: Kara karfin ciki,
‎Vitamin E da beta-carotene haka yanasa fata ta kasance lafiya da haske.

‎FADAKARWA MAI MAHIMMANCI.
‎Lokutan da Yak**ata ayi hattara da dabino, Masu fama da IBS, gudawa, ko matsananciyar matsalar hanji, Bayan cin Abinci mai nauyi sosai Airin Wadannan lokutan Arage yawan cin dabino.

‎ABDUSSAMAD ADAM – FUNTUA
‎Director, Raudatul Haq Islamic Medicine & Research Center
‎📞 08033319466







10/05/2026

ALAMOMIN SHAFAR AL-JANI, Bambancin tsakanin sihiri da shafar Aljani, Manyan bayanai gameda matsalar iska.....

Hashtags:

28/04/2026

Alamomin shirin, na jiki, hankali da ruhi, matakin kariya na gaggawa daga umarnin musulunci.......

07/04/2026

‎AMFANIN (RUMMAN) DA MAGUNGUNANSA A MUSULUNCI.

‎Rumman na daga cikin yayan itatuwa masu dimbin tarihi da daraja tun kafin zuwan Musulunci, Masana tarihi da bincike sun tabbatar da cewa an dade ana amfani dashi wajen abinci da magunguna. A harshen Turanci ana kiransa Punica granatum. Asalin noman rumman yasamo tushe ne daga kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman Iran da Turkmenistan, daga nan kuma ya bazu zuwa sassan duniya da dama saboda amfaninsa ga lafiyar dan Adam.

‎Tun kafin zuwan Musulunci, al’ummomi daban-daban suna amfani da rumman a fannoni da dama, musamman wajen hada magunguna, domin yana dauke da sinadarai masu matukar amfani ga jiki.
‎Kalmar rumman tana da tsohon asali a harsuna daban-daban. Ana ganin an samo ta ne daga tsohuwar kalmar Masaranci (rumn) da kuma asalin Farisanci, wanda hakan ke nuna dadadden tarihinsa a duniya.

‎(RUMMAN) A ALQUR’ANI DA HADISI.

‎Allah Madaukakin Sarki ya ambaci rumman a cikin Alqur’ani mai girma, inda Ya ce: “A cikinsu akwai yayan itatuwan dabino da rumman.” (Suratul Rahman)
‎Haka kuma Annabi Muhammad (SAW) yayi wasiyya da cin rumman, inda aka rawaito yana cewa: “Kuci rumman tare da kitsensa (bawon cikinsa), domin yana tsaftace ciki kuma yana karfafa shi).
‎Hakanan Sayyiduna Ali (R.A) yace: “Kuci rumman da kitsensa, domin yana tsarkake ciki.” An kuma rawaito daga Sayyiduna Abubakar (R.A) cewa: “Duk wanda yaci rumman, shaidan zai nisance shi tsawon kwana arba’in.” Wannan ruwayoyi suna nuni da cewa rumman ba abinci kawai ba ne, magani ne ga jiki da ruhin dan Adam.

‎AMFANIN RUMMAN GA LAFIYAR JIKI.
‎rumman yanada matukar amfani ga Lafiyar Ciki, Yana wanke ciki daga datti da cututtuka, Yana magance gudawa da ciwon ciki, Kitsen rumman (bawon ciki) na da tasiri wajen dakile kwayoyin cutar fata,
‎Lafiyar Fata da Baki, Bawon rumman na dauke da antioxidants da astringents
‎Yana taimakawa wajen magance: Gyambon fata, Ciwon baki, Matsalolin hakora, Ƙarfafa Kwakwalwa da Tarbiyyar Yara.
‎Bugu da kari shine Annabi Muhammad (SAW)

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Wuse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Any We H Were
Wuse