Abu Aseem Assalafiy

Abu Aseem Assalafiy

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abu Aseem Assalafiy, Health/Beauty, Kaduna, Zaria.

18/02/2022

•DALILIN DAKE JAWO AZABAR ƘABARI•

Ankarɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (RA) Yace: Wata rana Manzon ALLAH {s.a.w} ya wuce ta gurin wasu ƙaburbura guda biyu 2,

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} Yace:
Haƙiƙa waɗannan ma'abota ƙaburbura, ana yi musu azaba acikinsa, amma fa bawai ana yi musu azaba bane da wani babban zunubi ba, (kodai shima laifi ne).

Amma shidai ɗayansu yakasance baya suturcewa baya kuma tsaftace al'aurarsa idan yayi fitsari.

Amma shi kuwa na biyun yakasance yana tafiya da yaɗa jita-jita wato anna-mimanci.

Daganan sai Manzon ALLAH {s.a.w} yasa aka kawo masa wata itaciyar Dabino sai ya karɓa ya tsagata biyu 2, saiya kafa (Dasa) kowane tsagi ɗaya ajikin kowanne ƙabari ɗaya.

Daganan sai sahabbai s**ace dashi meyasa ka aikata haka ya Ma'aikin ALLAH {s.a.w}?

Sai yace: Nayi hakane saboda mai yiwuwa ALLAH ya sauƙaƙa musu azabar ƙabarin kafi itatuwan su bushe.

DARASI:

Wannan Hadisi yana mana nuni da illar bayyanar da al'aura, mace ko namiji, musamam maza masu fitsari akan hanya.

Da kuma illar yin fitsari aƙiyin tsarki, da kuma masifar da hakan yake jawowa acikin ƙabari.

Da kuma sakamakon mai ɗaukar magana daga wani guri izuwa wani guri,

Akwai wanda dagajin magana zai ɗauka yakai gaba,

Wani kuma har a social media saiya watsata kawai dan baisan masifar da zai jawowa kansaba a ƙabari.

ALLAH kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya.
Ameen...

01/02/2022

BABU RANAR HIJAB A MUSULUNCI KO MAKON HIJAB...

Musulunci Addini ne mai tsari kammalle wanda bayada buƙatuwa zuwa ga ƙari ko ragi. Na ga kafafen sada zumunta da yawa sunata sako hutunan wasu mata sanye da hijabai iri daban daban ban sani ba matan musulmai ne ko ba musulmai bane, anyi rubutu da sunan murna da farin ciki zagayowar ranar hijabi ta duniya.

Asalin wannan tunani ne na wata musulma dake zama a ƙasar Amurika irin yadda ake musguna mata saboda sanya HIJAB ɗin da takeyi a gurin aiki da wasu guraren, sai wannan tunanin yazo mata na saka daya ga watan Fabrairu a matsayin ranar zagayowar hijab sai kuma tayi kokari wajen tallata wannan tunanin nata ga wasu mata na duniya da ƙungiyoyi masu jingina kansu zuwa ga Musulunci, misali ƙungiyar ƴan ikhwan, M.S.S, Fonwan da sauran su kuma s**a karba abun hannun biyu biyu suna yaɗawa duk shekara a 01/02 .

HUKUNCIN WANNAN ƘAGGAGEN BUKI A MAHANGAR MALAMAN MUSULUNCI
Duk wata rana ko mako ko wani lokaci da aka saka ko aka ayyana domin yin murna ko farin ciki da zagayowarta idan ba wanda musuluncin ya ayyana ba ko ya saka to wannan rana baya halasta shi ne ake kira bidi'a.

قال الشيخ ابن عثيمين رحمه الله :
" إن كل الأعياد التي تخالف الأعياد الشرعية كلها أعياد بدع حادثة ، لم تكن معروفة في عهد السلف الصالح ، وربما يكون منشؤها من غير المسلمين أيضاً ، فيكون فيها من البدعة مشابهة أعداء الله سبحانه وتعالى ، والأعياد الشرعية معروفة عند أهل الإسلام ، وهي عيد الفطر، وعيد الأضحى ، وعيد الأسبوع ( يوم الجمعة ) وليس في الإسلام أعياد سوى هذه الأعياد الثلاثة " انتهى من " مجموع فتاوى ابن عثيمين " (2/301)

Ashshiekh Ibnu Uthaimeen Raحimahulllah yace: " lallai duk idin da suke saɓawa idin Shari'a dukkan su bidi'a ne ƙagaggen abu ne, bata kasance sananna ba a lokacin magabata na kwarai, sau da yawa ya ke kasancewa masu rayata (Ranar) ba musulmi bane kuma, sai daga
cikinta bidi'a ta kasance kamam ceceniya ne da makiya Allah Tsalki ya tabbata garesa madaukakin sarki, idin Shari'a sanannu ne a gurin ma'abuta musulunci, sune : IDIN BUDA BAKI

28/01/2022

Duk yadda ka kai da zama mutumin kirki, a wurin wani arne kake😂, Kawai ka rabu da mutane ka nufi Allah da ayyukanka👈

25/01/2022

Ranar mutuwar mumini👈itace rana mafi farin ciki gare shi da annashuwa
Ya Allah ka sanya mu daga cikin muminan bayinka🙏

24/01/2022

Kai dai kayi komai dan Allah, ka sani mutane zasu iya raba ka da komai ,amma baza su iya raba ka da allah ba sai in kaso

24/01/2022

Da kai nake yi mai karatu👈

Allah ya gafarta maka bayan mutuwar ka sannan ya shigar 👉aljannah🙏🙏🙏

23/01/2022

Azabar kabari
zapin pitar rai
Duhun kabari
mummunar karshe

Ya Allah ka tsare mu daga dukkan su🙏🙏🙏

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kaduna
Zaria