Lafiya Ni’ima

Lafiya Ni’ima

Share

Lafiya ni’imace da Allah yayi mana. Zamu dinga aiko muku abubuwa da dama a kullum domin lafiyarku.

24/09/2026

Kada a manta garabasa! Azumin ayyamul beed wannan wata. Yau, gobe, da jibi! Riba biyu: ga lada ga lafiya!

27/07/2026

Wa yasan wani abinci mai arha a Nijeria (kusan kyauta), amma yana da lafiya da furotin (protein) fiye da nama?

26/07/2026

Ga lada, ga lafiya: Ayi niyyar azumi gobe zuwa alhamis, Wanda yayi daidai da 13-15 na safar, da kuma azumin sunna na alhamis.

16/06/2026
20/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 27:
A rage lodi lokacin buɗa baki don a samu cikakken fa'idar azumi na lada da lafiya. A sha ruwa lafiya.

17/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 26
Daga gobe ne fa! Ayi azumin taran farkon Dhul hajj! Ga lada ga lafiya!

11/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 25
Aci abinci daidai gwargwado idan anji yunwa na gaske. Sauran nau'ika tara na yunwar bogi kuma, ayi ƙoƙari ayi maleji, in za'a iya ayi mirsisi, ba sai anci ba.

10/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 24:
Ku banbance yunwar gaske, me buƙatar aci abinci, da sauran nau’ikan yunwa!

04/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 23
Kuyi ƙoƙari kuna motsa jiki nau’in miƙa/ lanƙwasa (stretch and flexibility) sau ɗaya a sati, kamar irin na wannan bidiyon. Akwai shi a manhajoji dayawa. Wannan screen recording ne daga waya ta a manhajar “pacer”. Akwai su iri daban-daban a yanar gizo.
Idan ba’a mantaba, a shawara ta 8, mince ku dage, ku doge akan motsa jiki nau’i uku a ko wane sati: 1.Aerobics,
2. Nau’in gina ƙwanji, da
3. Lanƙwasa.
Aeorobics sau biyu, nau’in gina ƙwanji sau biyu , da kuma lanƙwasa sau daya zai wadaceku.
Kamar yadda jikinka yake bukatar manyan nau’ikan abinci uku kafin ka samu “balanced diet”, haka shima motsa jiki ana bukatar nau’i uku a sati.

01/05/2026

SHAWARAR LAFIYA TA 22
Yau juma'a , haji babbar rana. A yawaita salati ga manzo ﷺ.
Shawarar mu ta lafiya kowace juma'a, daga hadisin manzo ﷺ muke kawowa.
Kuyi aiki da wannan ingantaccen hadisi, ku samu lada, ku samu lafiya!

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Bisha?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Bisha

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lafiya Ni’ima posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Bisha.