Rayuwa da waraka daga ciwon sukari

Rayuwa da waraka daga ciwon sukari

Share

Zamu dinga bada shawarwari daga masana ciwon s**ari ta yadda za’a warke ko a samu saukin ciwon s**ari

Photos from Rayuwa da waraka daga ciwon s**ari's post 27/03/2026

GWAIBA (GUAVA) YANA DA FA’IDA GA LAFIYA SOSAI MUSAMMAN MASU CIWON SUKARI

'Yan Najeriya, a fahimtata, guava yana ɗaya daga cikin mafi kyawun 'ya'yan itatuwa a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Yana da arha, ana samunsa sosai, yana da daɗi, yana da ƙarancin s**ari, yana da yawan furotin/fiber in ka kwatanta shi da sauran 'ya'yan itace. , bugu da kari, yana da wasu kyawawan abubuwan gina jiki da fa'idodin lafiya da aka lissafa a cikin waɗannan bayanan.

03/02/2025

*TAMBAYA TA 3 AKAN AZUMI DA CIWON SUKARI: WANE ME CIWON SUKARI NE YA KAMATA YA AJIYE AZUMI?*
Kamar yadda bayani yazo a baya, azumi yana da fa'idoji da mutum zai iya samu ta bangaren lafiya idan ya yi, haka kuma yana iya zuwa da wasu illoli ga mai ciwon s**ari.
Likitoci suna la'akari da abubuwa da dama wajen bada shawara akan mutum yayi azumi ko kada yayi. Amma a jumlace, galibin masu ciwon s**ari suna iya yin azumi lafiya lau, musamman idan s**a ɗauki matakan rage haɗarin azumi da ciwon s**ari, waɗanda zamu yi bayani akansu a tambaya ta gaba in shaa Allah.
Wasu abubuwanda suke ƙara yiwuwan samun matasala ga mai ciwon s**ari idan yayi azumi sune:
1. Nau'in ciwon s**ari: Anfi samun matsala a ciwon s**ari nau'i na 1 (type 1) musamman idan ana anfani da allurar insulin sau da yawa a rana.
2. Rashin daidaituwar s**ari (poor control), musamman idan HbA1c ya wuce 9%.
3. Irin maganin da ake anfani da su. Wasu magunguna irin su allurar insulin ko ƙwayoyi masu saka raguwar s**ari a jini sosai (hypoglycemia).
4. Kasancewar wasu cututtuka kamar su ciwon hanta ko ƙoda a tareda mutum.
5. Rashin jin alamun raguwar s**ari a jini (hypoglycemia unawareness).
6. Samun ƙarancin s**ari (hypoglycemia) a baya, musamman ƙasa da wata uku.
7. Rashin na'urar gwada s**ari, musamman ga wanda ke anfani da allurar insulin.
8. Kwanciya a asibiti saboda yawan s**ari (hyperglycemia).
9. Juna biyu.
10. Yanayin aikin mutum, idan ya kasance me aikin karfi ne.
11. Samun matsala a azumi a baya.
12. Yawan lokacin da akeyin azumin (wasu kasashe ana azumi sama da awa 16 misali).
13. Yanayi (weather).
Likita zai yi anfani da irin waɗannann bayanan game da ciwon s**arin mutum wajen bada shawara akan yayi azumi, ko kada yayi. Kaima kana iya samun haske akan wannan kafin shawara da iktanka.
Allah ya sa mu dace.

02/02/2025

TAMBAYA TA 2 AKAN AZUMI DA CIWON SUKARI: MENENE FA’IDA KO ILLAR AZUMI GA MAI CIWON SUKARI?

Binciken kimiyya sun
tabbatarda wasu fa’idoji da mutum zai iya samu idan yayi azumi, ko yana da ciwon s**ari ko babu.
Wasu daga ciki sune:
1. Raguwar hawan s**ari a jinin mutum.
2. ⁠Raguwar kitse (kwalesterol) a jini, wanda ya addabi yawancin masu ciwon s**ari.
3. ⁠Raguwar tumbi.
4. ⁠Rage kiba
5. ⁠Da sauransu.
Akwai kuma illolin da ke iya samun mai ciwon s**ari idan yayi azumi. Wadanda s**a fi shahara sune:
1. Karancin s**ari a jini (hyooglycemia).
2. ⁠Hauhawar s**ari a jini(hyperglycemia).
3. ⁠Suma na “keto-acidosis”.
4. ⁠Raguwar ruwa a jiki (dehydration).
Aikin likitanka ne ya duba yanayin ciwon s**arinka yaga shin kai irin wadanda zasu samu fa’idar azumi ne, ko wanda ke da hadarin samun illolin da muka lissafa? Ko da yake aikin likitanka ne ya baka shawara ko kayi azumi ko karkayi, gobe in shaa Allahu, zamu yi bayanin me likitoci suke la’akari da su wajen yanke hukuncin ko mai ciwon s**ari yayi azumi ko a’a.
Ga masu bukata a kimiyyance, ga wani bincike da ya tattara kusan duk binciken kimiyyanda akayi akan ciwon s**ari da azumi.

*Morales-Suarez-Varela M, Collado Sánchez E, Peraita-Costa I, Llopis-Morales A, Soriano JM. Intermittent Fasting and the Possible Benefits in Obesity, Diabetes, and Multiple Sclerosis: A Systematic Review of Randomized Clinical Trials. Nutrients. 2021 Sep 13;13(9):3179. doi: 10.3390/nu13093179. PMID: 34579056; PMCID: PMC8469355.*

30/01/2025

TAMBAYOYI DA AMSOSHI 30 AKAN AZUMI DA CIWON SUKARI

Yau saura kimanin wata daya a fara azumin Ramadan in shaa Allah . Allah ya nuna mana da rai da lafiya. Allah ya bamu ikon yin ibada karbabbiya. Allah ya samu çıkın ‘yan tattu daga wutar jahannama.
Daga yau in shaa Allah, zamu dinga amsa tambaya daya kullum akan azumi ga mai ciwon s**ari. In shaa Allah zamu amsa tambayoyi talatin zuwa Ramadan.
Muna da tambayoyi da mutane suke yawan yi. Amma Idan kunada tambaya, zaku iya turowa.

*Tambaya ta 1 akan azumi da ciwon s**ari: Ina da ciwon s**ari, inyi azumi ko na ajiye azumin?*
*Amsa*:
Amsa wannan tambaya yana da harshen damo, zai iya zama eh ko a'a. Akwai abubuwan da likitoci suke la'akari dasu kafin su bada shawarar ayi azumi ko a'a.
Azumi yana da fa'iodoji da me ciwon s**ari zai samu in yayi, amma kuma akwai wasu matsaloli da ke iya samun mutum me ciwon s**ari idan yayi azumi.
Masana sun bada shawarar cewa ko wane me ciwon s**ari ya tuntubi likitansa wata 2-3 kafin azumi don a bashi shawarwarin da s**a dace dashi.
A tanbaya ta biyu gobe in shaa Allah, zamu dubi fa'idoji da matsalolin azumi ga me ciwon s**ari. A tambaya ta uku kuma zamu dubi wane me ciwon s**ari ne ya kamata ya ajiye azumi, wanne ne kuma zai iya yin azumin?

26/11/2024

Rashin bacci yana kara sinadaran “ hormones” a jikin mutum irinsu “cortisol” da “cathecolamines” wadanda şu kuma suke sa s**ari ya hau a jiniin me ciwon s**ari. Saboda haka , a samu wadataccen bacci, zai taimaka wajen rage hawan s**ari a jinin me ciwon s**ari.

Abubuwa Goma Masu Haifar da Matsalar Rashin Barci (Insomnia)

1. Yawan gajiya ko fargabar wani abu (anxiety)

2. Ciwon tunani (depression)

3. Rashin tsayar da takamaiman lokacin zuwa kwanciya da lokacin tashi

4. Yawan amfani da wayar hannu ko kwamfuta kafin a kwanta

5. Yin atisaye mai bukatar karfi sosai

6. Sha ko cin abubuwa masu sinadarin caffeine kamar coffee, chakulet, lemuka masu ƙara kuzari (energy drinks) da makamantansu

7. Shan wasu magunguna na asibiti kamar na magance ciwon damuwa musamman lokacin da aka fara sha.

8. Matsalar asthma da sauran matsaloli masu kawo yawan tari cikin dare

9. Matsalar numfashi (haƙi) kamar daga ciwon zuciya

10. Kwanciya a wajen da akwai haske sosai ko kuma ana yawan surutu

A duba rubutunmu na gaba domin ganin yadda za a magance matsalar.

Likita24

30/10/2024

Bincike akan mutane wajen dubu casa’in ya nuna cewa motsa jiki yana rage hadarin kamuwa da cututtuka fiye da 250!A motsa fa!

19/10/2024

Labarin lafiya mai dadi: Bincike ya nuna ko sau 1 kake motsa jiki a sati, akwai fa’ida; matukar ya kai awa daya da rabi. Duba comment section.

14/07/2024

Binciken masana ya alaqanta hasken dare da ciwon s**ari. Dama annabinmu (SAW) ya koya mana kashe fitila da dare. Duba comment

Gabatarwa 06/07/2024

Gabatarwa Assalaamu akaikum. Sunana Bappa Adamu. Ina bincikene akan yanayin ciwon s**ari a cikin jama'a masu jin Hausa. Zanyi muku tambayoyi akan wannan. Baza'a sanarda jama'a amsarku ba saidai a jumlace. Wanda yakeso za'a turo masa shawarwari bisa amsohinda ya bayar. Zai ɗau mintoci wajen bada amsoshin. Tam...

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Bisha?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Bisha

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rayuwa da waraka daga ciwon sukari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Bisha.